Najeriya a Yau

10 Episodes
Subscribe

By: Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
Today at 6:00 AM

Send us a text

Cututtuka da dama suna Kamari a Najeriya wanda a mafi yawancin lokuta ma wadanda ke dauke da irin wadannan cututtukan basu da masaniyar suna dauke da su.


 Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan dake tabbatar da lafiyar bil’adama.


 Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace cutar Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan dake sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya.


Dalilin Karyewar Farashin Shinkafa A Wasu Kasuwannin Najeriya
Last Tuesday at 5:00 AM

Send us a text

Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, daya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan kasar.


Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi – shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ka iya haddasawa a rayuwar talaka?


A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari.


“Dalilan Da Suka Sa Muke Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyya Mai Mulki”
Last Monday at 5:00 AM

Send us a text

Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya shekar da ’yan siyasa daga banarori daban-daban suke yi.


A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ta jawo diga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaben 2027.

Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan Najeriya suke kokawa da yadda ake gudanar da mulki a kasa da yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa...


Dalilan Da Suka Sa Zazzabin Cizon Sauro Ba Ya Jin Magani
Last Friday at 5:00 AM

Send us a text

Zazzabin cizon sauro, wato malaria, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma hadari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya.


Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta malaria kan sake kamuwa da ita bayan ya warke.
Ko me ya sa magungunan zazzabin cizon sauro suka daina aiki a jikin mutane?


Wannan batu shirin Najeriya A Yau zai duba yayin da ake bikin Ranar Malaria ta...


Hanyoyin Amfani Da Kafafen Sada Zumunta Wajen Habbaka Kasuwanci
04/24/2025

Send us a text

Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da kananan sana’oi, wanda alumma ke dogaro dasu don biyan bukatun su na yau da kullum.


Irin wadannan sana’oi sun hada da saka, jima, balangu, suyan kosai ko masa da dai sauran sana’oi da alumma keyi.
A da can baya irin masu wadannan sana’a sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da abun da suke sana’antawa ko kuma wadanda suka samu a yayin da suka dauki tallan sana’ar tasu.
Sai dai a wannan zam...


Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
04/22/2025

Send us a text

Ko kun san tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shuaban Kasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa?


Kundin na Tsarin Mulkin Kasa ne dai kundin dokoki mafi karfi a Najeriya wanda ya kunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shuggabanni da ma al’ummar kasa.
Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gudanar da dukkan al’amuran kasa, haka Kundin ya ayyana karfin ikon da kowane shugaba yake da shi, da iyakar...


Me Ya Sa Matsalar Tsaro “Ta Gagari Gwamnati” A Najeriya?
04/21/2025

Send us a text

A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga ɗimbin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu matsalolin na ƙara Kunno Kai.


Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar kalubale iri-iri kama daga hare-haren da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, zuwa ga sabbin kashe-kashe a wasu garuruwan jihohin Filato da Binuwai sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta bulla  a jihar Kwara.
To ko mene ne ya haddasa...


Sabbin Dabarun Hana Matasa Aikata Laifuffuka
04/18/2025

Send us a text

Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. 
Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su.


’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da kwacen waya da fyade kai har ma da satar mutane don kudin fansa a tsakanin matasa.


Ko yaya wannan dabara take...


Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?
04/17/2025

Send us a text

Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin.


 Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun.


Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa l...


Dalilan Rikice – Rikice A Jihar Filato
04/15/2025

Send us a text

A yanzu haka, al’ummar jihar Filato na cikin fargaba da tashin hankali sakamakon jerin hare-haren da suka afku a wasu sassan jihar, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu, wasu kuma suka tsere daga muhallansu.


Ko mene ne dalilin sake fitowar rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin da ake ganin an fara samun zaman lafiya?


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan rikice rikicen Jihar Filato da dalilan aukuwar su.