Najeriya a Yau

10 Episodes
Subscribe

By: Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Matakan Kauce Wa Yaɗuwar Cutuka A Makarantu Saboda Tsananin Zafi
Today at 5:00 AM


Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje
Yesterday at 5:00 AM

Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa

Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can.

Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.


Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya
Last Friday at 5:00 AM

Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya.

Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka?

Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.


Me Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Ƙi Karya Farashi Duk Da Karyewar Dala?
Last Thursday at 5:00 AM

Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi.

Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa.

Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.


Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC?
04/16/2024

An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba.

Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa.

To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.


Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi
04/15/2024

Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata.

Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba.

Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.


Shin Ya Dace Mace Ta Fara Sitta-Shawwal Kafin Biyan Bashin Ramadan?
04/12/2024

Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal?

Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi?

Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.


‘Da Ƙyar Muka Iya Cefanen Sallah Bayan An Sauko Idi’
04/11/2024

Matsin rayuwa yana daga cikin abin da ya hana mutane da dama yin shagali da wannan karamar Sallah.

Wasu ma basu iya yin cefanen Sallah na abincin da za a ci ballantana sabbin dinkuna.

Shirin Najeriya a Yau ya zagay wasu jihohu domin yadda mutane suka yi Sallah cikin matsin rayuwa.


Wani Tela Ya Tsere Saboda Rashin Gama Ɗinkunan Sallah
04/09/2024

Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu.

Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo!

Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.


Mutanen Da Aka Haramtawa Cin Zakkar Kono
04/08/2024

Shin a wane lokaci aka yi umarnin fitar za Zakkar Fidda Kai?

Malamai sun ce wannan Zakka tana da matukar mahimmanci ga masu hali kuma akwai lokacin da aka kayyade a fitar da ita; in ba haka ba kuma ta zama sadaka.

Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan fidda Zakatul-Fitr da mutanen da aka haramtawa cin ta.